Gwamnan APC ya bawa sabbin hadimansa mamaki, ya debi su zuwa hedikwar Boko Haram

Gwamnan APC ya bawa sabbin hadimansa mamaki, ya debi su zuwa hedikwar Boko Haram

Zababben gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagan Umara Zulum, ya yi taro na farko da sabbin hadimansa da manyan jami'an gwamnati a garin Damasak, hedikwar karamar hukumar Mobbar, tsohuwar daular kungiyar Boko Haram.

An shirya taron ne domin sabbin kwamishinoni, masu bayar da shawara, sakataren gwamnati, da sauran manyan jami'an gwamnatin jihar Borno.

Da yake gabatar da jawabin bude taro, gwamna Zulum ya bayyana cewa ya zabi gudanar da taron a Damasak ne domin tuna wa sabbin masu rike da mukamin da ya nada cewa ba jin dadi ne a gabansu ba.

"Bisa al'ada kowa ya san cewa an fi gudanar da irin wannan taro a muhalli na jin dadi. Duk da yin hakan ba laifi bane, amma ya kamata kowa ya gudanar da taronsa cikin yanayin da yake.

DUBA WANNAN: Amarya ta fadi sumammiya ranar biki bayan ta gano wani boyayyen sirri a kan angonta

" Kowa ya san yanayin da muke ciki a jihar Borno ba na jin dadi bane ko more rayuwa, wannan ba sai na tuna muku ba.

"Zan iya gudanar da wannan taro a Maiduguri, ko na kai shi Abuja ko wurin shakata wa na Obudu da ke jihar Kuros Riba, amma na fi son mu yi aiki da zahiri, a cikin yanayin da jama'ar mu ke ciki, hakan zai bamu damar sanin gaskiyar halin da muke ciki da kuma fuskantar aikin da ke gabanmu," a cewar Zulum.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel