Yanzu-yanzu: Buhari zai shilla kasar Rasha gobe tare da gwamnoni 3 da ministoci 4

Yanzu-yanzu: Buhari zai shilla kasar Rasha gobe tare da gwamnoni 3 da ministoci 4

A ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba, shugaba Muhammadu Buhari zai tafi kasar Rasha domin halartan taron kwana uku na alakar Afrika da Rasha a birnin Sochi, na kasar. Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana.

Bisa jawabin da ya saki, za'a gudanar da wannan taro ne tsakanin ranar 23 da 25 ga Oktoba, kuma za'a tattauna kan fadada hanyoyin samar da tsaro, kasuwanci da hannun jari, kimiya da fasaha da arzikin iskar gas.

Shugaba Buhari zai tafi da gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, Bello Matawalle na jihar Zamfara da Kayode Fayemi na jihar Ekiti.

Hakazalika, akwai ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama; ministan hannun jari, Adeniyi Adebayi; ministan ma'adinai, Olamilekan Adegbite da ministan man fetur, Temipre Sylva.

Jawabin yace: "A ganawar, shugaba Buhari zai gana da shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin domin karfafa alaka kan tsaro, kasuwanci da hannun jari, arzikin iskar gas."

Legit.ng ta fahimici cewa wasu shugabannin kasashen Afrika zasu halarci taron .

Kana za'a yi taron manyan yan kasuwan Afrika da na Rasha domin hadin kai da cigaba.

A makonnin kusa, shugaba Buhari ya halarci taron TICAD7 a kasar Japan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel