An bayar da belin mai cibiyar azabtarwa ta Kaduna 'yan sa'o'i kadan bayan kama shi

An bayar da belin mai cibiyar azabtarwa ta Kaduna 'yan sa'o'i kadan bayan kama shi

Rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna ta bayar da belin Malam Lawal Yusuf Maduru, mai cibiyar azabtar da jama'a, da aka kama a Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa an saki Malam Maduru ne jim kadan bayan jami'an 'yan sanda sun kai samame gidan da yake daure kangararrun yara da ke Kwanar Gurguwa a karamar hukumar Rigasa, inda suka kama shi.

Daily Trust ce ta fara wallafa labarin cewa jami'an 'yan sanda sun kai samame cibiyar da yammacin ranar Asabar.

A hirarsu ta wayar tarho, Malam Maduru ya tabbatar wa da Daily Trust cewa jami'an 'yan sanda sun sake shi jim kadan bayan sun kama shi, kuma yana gida tare da iyalinsa.

"Hakane, an sake ni bayan kamawar da aka yi min, yanzu haka ina gida tare da iyalina," a cewar Malam Maduru.

Kazalika, Daily Trust ta bayyana cewa jama'ar unguwa sun barke da murna a ranar Asabar da yamma bayan Malam Maduru ya dawo gida bayan da farko jami'an 'yan sanda sun tafi da shi bayan sun rufe cibiyar da yake daure mutane da sunan gyaran tarbiya.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo, ya tabbatar da bayar da belin Malam Maduru tare da bayyana cewa an bayar da shine a kan beli bisa sharadin cewa zai koma ranar Litinin.

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel