Gwamnatin Najeriya za ta samu aron Dala Biliyan 3 daga bankin Duniya

Gwamnatin Najeriya za ta samu aron Dala Biliyan 3 daga bankin Duniya

A kokarin da gwamnatin tarayya ta ke yi na ganin matsalar wutar lantarki ya zama tarihi a Najeriya, mun samu labari cewa Najeriya ta yi nasarar samun wasu bashin kudi da ta ke nema.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar The Cable, babban bankin Duniya ya amince da rokon da Najeriya ta gabatar na samun aron Dala biliyan 3 domin gyara wutar lantarki.

Babban bankin ya yi na’am da kokon barar gwamnatin tarayyar inda aka amince da ya ba ta wannan kudi da nufin fadada hanyoyin raba wutar lantarki inji babbar Ministar kudin kasar.

Ministar kudi da kasafi da tsare-tsare, Misis Zainab Ahmed Shamsuna, ta tabbatar da wannan a lokacin da ta ke zantawa da Manema labarai dazu a Ranar Lahadi, 20 ga Watan Oktoba 2019.

KU KARANTA: Shugaba Buhai ya yabawa Kabilar Yarbawa a Najeriya

Zainab Ahmed ta fadawa ‘yan jarida inda Najeriya ta kwana ne a taron da ta ke ta faman yi da bankin Duniya da kuma hukumar IMF mai bada lamuni a Duniya game da harkar lantarki.

Rahoton na Jaridar The Cable ya ce Ministar ta bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta yi amfani da wannan biliyoyin daloli ne wajen gyara sha’anin wuta wanda ya zama ala-ka-kai a kasar.

Dazu nan mu ka ji cewa Bankin Duniya ya ba Najeriya kudi domin magance matsalar wuta. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake cin wasu makudan bashi domin inganta lantarki.

Tun kwanaki Ministar kasar ta sanar da jama’a cewa su na kokarin tattaunawa da babban bankin na Duniya domin ganin gwmnatin Buhari ta samu aron kudin da zai kawo karshen wahalar wuta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel