Atiku Abubakar ya taya Omokri murna, ya nemi a ceto Leah Sharibu

Atiku Abubakar ya taya Omokri murna, ya nemi a ceto Leah Sharibu

‘Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar, ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta kara kokari wajen kubutar da Leah Sharibu wanda ta dade ta na hannun Boko Haram.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi kira ga shugaban da ke fafatukar tafiyar #FreeLeahSharibu watau Reno Omokri, ya kara kokari wajen gwagwarmayar da yake yi.

Atiku ya yi wannan jawabi ne ta bakin Hadiminsa na yada labarai lokacin da yake taya Fasto Reno Omokri murnar wata kyauta da ya samu a kasar waje daf da karshen wannan shekara.

A Ranar Asabar 2 ga Watan Nuwamban 2019 ake sa rai cewa wata Mujallar mako-mako ta kamfanin fina-finan Hollywood da ke Garin California a kasar Amurka za ta karrama Omokri.

KU KARANTA: Atiku da tsohon Shugaba Jonathan sun aikawa Gowon sakon murna

Gajeren jawabin na Alhaji Atiku Abubakar yana cewa: “Iyali na da ni kai na mu na taya ka murna a wannan lokaci na musamman, tare da rokon Ubangiji ya kara maka lafiya da basirar yin daidai.”

A jawabin mun fahimci cewa Omokri ya ziyarci kasashe fiye da 35 a Duniya ya na neman goyon bayansu wajen ganin an kubuto da Leah Sharibu daga hannun ‘Yan ta’addan Boko Haram.

Omokri wanda ya yi aiki a matsayin Hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya ziyarci dutsen Mount Everest da ke kasar Nepal domin jawo hankalin Duniya game da batun.

A farkon 2018 Boko Haram su ka sace wasu Yaran makaranta fiye da 100 a Garin Dapchi, daga baya an dawo da su amma aka cigaba da tsare Leah Sharibu saboda ta ki karbar addin Musulunci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel