Jonathan da Atiku sun taya Yakubu Gowon murnar cika shekara 85, sun kira shi 'Dan kishin-kasa

Jonathan da Atiku sun taya Yakubu Gowon murnar cika shekara 85, sun kira shi 'Dan kishin-kasa

A jiya ne mu ka ji cewa tsohon shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya aika sakon taya murna na musamman ga Janar Yakubu Gowon bayan ya cika shekaru 85 a Duniya.

A cewar Goodluck Jonathan, Gowon jajirtaccen shugaba ne wanda ya jagoranci Najeriya da daraja da kishi da kuma soyayya. Jonathan yace har gobe Najeriya ta na cin moriyar Dattijon.

Sakon Goodluck Jonathan wanda ya mulki Najeriya daga 2010 zuwa 2015 ya yi wa Janar Gowon addu’ar cigaba da samun kwari da lafiyar shekaru masu albarka a yayin da ya cika 85.

"Ina taya ka murna da sauran Masoya a daidai lokacin da ka ke bikin murnar cika shekaru 85.'"

Jonathan yace Gowon ya rike Najeriya a wani lokaci mai wahalar sha'ani. Tsohon shugaban ya gamu da rikicin yakin basasa ne a lokacin ya na kan mulki a shekarun 1966 zuwa 1975.

KU KARANTA: Buhari ya kira Gowon gwarzo bayan ya cika shekara 85

“Shekaru bayan barin ka ofis, kishin ka da kaunar kasar ka bai canza ba domin ka cigaba da kokarin yi wa Najeriya hidima da addu’o’i domin ganin ta cigaba.”

“A matsayin ka na Dattijo, ka tsaya tsayin daka na ganin an samu zaman lafiya a Najeriya.”

"A madadi na da Iyali na, ina maka fatan karin lafiya da zaman lafiya yayin da ka ke murna."

Inji @GEJonathan

Shi ma Alhaji Atiku Abubakar ya aika na sa sakon taya murnar ga Janar Yakubu Gowon a shafinsa na sada zumunta na Tuwita. Atiku ya aika wannan sako ne a Ranar 19 ga Oktoba.

Tsohon mataimakin shugaban kasar kuma ‘dan takarar PDP a zaben 2019, ya roki Ubangiji ya karawa Gowon shekarun cigaba da yi wa Najeriya hidima kamar yadda ya saba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel