Buhari ya yabawa mutanen Yarbawa, ya kira su manyan Kabila

Buhari ya yabawa mutanen Yarbawa, ya kira su manyan Kabila

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya yabawa kabilar Yarbawa inda ya kira su manya. Shugaban Najeriyar yace Yarbawa mutane ne da su ke da kokarin fito da mutanen kwarai.

Muhammadu Buhari ya bayyana yadda Yarbawa su kayi kaurin suna wajen yi wa wadanda su ka yi fice daga cikinsu sakayya. Buhari ya bayyana wannan ne wajen nadin Odole Oodua na Ife.

Shugaban kasar ya yi wannan jawabi ne a matsayinsa na babban bako wajen nadin Kesington Adebutu a matsayin mai rike da sarautar Odole Oodua na kasar Ife wanda aka yi Ranar Asabar.

Mai martaba Ooni na Garin Ife watau Oba Adeyeye Ogunwusi, shi ne ya ba Kesington Adebutu wannan babbar sarauta. Shugaban kasa Buhari yana cikin wadanda aka gayyata wajen nadin.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, shi ne wanda ya wakilci shugaban Najeriyar a wajen bikin nadin sarautar. Aregbesola shi ne ya yi jawabi a madadin shugaban kasa a taron.

KU KARANTA: Akwai alamun Nicky Minaj za ta zama Amarya kwanan nan

Tsohon gwamnan yankin, Rauf Aregbesola, ya nuna cewa bai san wanda aka yi wa nadin ba sosai, amma ya nuna cewa babu shakka sarauta ce mai girma ya samu idan aka duba wadanda ya gada.

Kolawole Ajayi da tsohon Firimiyan kasar Kudu kuma jigon siyasar Najeriya, Obafemi Awolowo sun taba rike wannan sarauta a kasar. Wannan ya sa ake ji da wannan nadi na Odolen Ife.

An yi wannan nadi ne a jiya Ranar Asabar 19 ga Watan Oktoba. Iyalan wannan Attajiri; Caroline Adebutu and Aminat Adebutu su ma ba a bar su a baya ba inda aka yi masa nadin sarauta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel