Banbancin shekaru biyar a tsakani: Alakar da ke tsakanin Buhari da Mamman Daura

Banbancin shekaru biyar a tsakani: Alakar da ke tsakanin Buhari da Mamman Daura

Shugaban kasa, Muhammad Buhari, da Mamman Daura, sun kasace tamkar 'yan tagwaye (Hassan da Usaini) duk da kasancewar Mamman Daura ya girmi Buhari da kusan shekaru 5.

Buhari da Mamman Daura sun fara shakuwa ne tun daga yarinta bayan Buhari ya koma gidan Malam Daudu Daura, mahaifin Mamman Daura, bayan rasuwar mahaifinsa, kamar yadda BBC Hausa ta wallafa a cikin labarinta.

BBC ta ce majiyarta ta tabbatar mata da cewa ko a dangi kowa ya san ba a shiga tsakanin Buhari da Mamman Daura tun suna kanana.

Majiyar BBC ta sanar da ita cewa, "tun suna kanana suke tare koda yaushe. Karatun makarantar sakandire ne ya fara raba su na wani lokaci mai tsawo. Mamman Daura ya tafi wata makarantar sakandire a garin Okene, shi kuma Buhari ya tafi makarantar sakandire ta Katsina."

DUBA WANNAN: APC ta nada gwamnoni biyu daga arewa su jagoranci yakin neman zabe a Kogi da Bayelsa

Majiyar ta kara bayyana cewa Buhari da Mamman Daura sun kara haduwa a kasar Ingila, bayan inda bayan dawowarsu gida Najeriya alakarsu ta kara karfi.

Sai dai, duk da wannan tsohuwar alaka da ke tsakanin Buhari da Mamman Daura, wasu 'yan Najeriya na ganin baiken shugaba Buhari saboda har yanzu duk da ya zama shugaban kasa bai jefar da dan uwa kuma amininsa tun na yarinta ba.

Masu irin wannna ra'ayi, irinsu Dakta Abba Kari, na ganin cewa karfin iko da fada ajin da Mamman Daura ke da ita a gwamnatin Buhari ta yi yawa duk da kasancewar ba ya rike da kowanne mukami a gwamnati.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel