Buhari ya yi barazanar janye kwangilolin FG daga wasu jihohi

Buhari ya yi barazanar janye kwangilolin FG daga wasu jihohi

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi barazanar janye kwangilolin gwamnatin tarayya daga wasu jihohi inda gwamnatocin jihohin ba su bawa 'yan kwangila hadin kai ko wuraren da aka ki bawa 'yan kwangilan filayen da za suyi aiki.

Shugaban kasar ya yi wannan gargadin ne cikin wata sanarwa ta mai magana da yawunsa Garba Shehu ya fitar da madadinsa a ranar Asabar.

Shugaban kasar ya ce wasu garuruwa suna hana ruwa gudu ga 'yan kwangilan ta hanyar neman a biya su makudan kudi don filaye inda wasu har koran 'yan kwangilan da ma'aikata su ke yi daga filayen.

Ya ce rashin hadin kai da al'umma ba su bawa 'yan kwangilan yana janyo koma baya ga gwamnati a yunkurin ta na yi wa al'umma hidima.

DUBA WANNAN: Wata budurwa ta fadi aka rika yin zina da su a gidan 'azabtarwa' na Kaduna (Bidiyo)

Ya ce, "Muzgunawa 'yan kwangila da gwamnatocin jihohi ke yi ta hanyar neman a biya su makuden kudi na filaye ko wasu wurare da gwamnatocin jihohi ke hana 'yan kwangilan filaye dabi'a ce da ba za ta bari a yi wa al'umma ayyukan more rayuwa ba."

"Bugu da kari, 'yan kwangilan da aka kora sukan sake bukatar a basu wasu kudaden duk lokacin da suka dawo don cigaba da ayyukansu."

"Hana gwamnatin tarayya filaye don gudanar da aiki yana kawo cikas wurin aiwatar da ayyuka, ba adalci bane kuma a koma ana zargin gwamnatin tarayya da mayar da wasu al'umma saniyan ware a fannin yin ayyuka."

"A bangaren yi wa al'umma aiki, kamata ya yi dukkan gwamnatoci su hada kai domin ganin an inganta rayuwar al'umma ba tare da la'akari da banbancin jam'iyyun siyasa ba.

"Ba zai yi wu gwamnatin tarayya ta yi dai-daita ayyukan tsakanin jihohi ba idan wasu al'umma na jefa siyasa cikin lamarin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel