Yanzu-yanzu: Bayan sa'o'i 40, Zakin gidan Zoo na Kano ya koma keji da kansa (Bidiyo)

Yanzu-yanzu: Bayan sa'o'i 40, Zakin gidan Zoo na Kano ya koma keji da kansa (Bidiyo)

Zakin da ya kwace a gidan Zoo na jihar Kano ya koma cikin kejinsa da kansa bayan sa'o'i 40 ana fafutuka tun ranar Asabar.

Manajan gidan Zoon, Said Gwadabe Gwarzo, ya bayyanawa maneme labarai da safiyar Litinin cewa "zakin ya koma cikin kejinsa da kansa cikin dare."

Legit.ng ta samu labarin cewa Zakin ya ki shiga kejin ne bayan dawowa daga wani baja kolin dabbobin dajin da akayi a jihar Nasarawa.

A daren jiya mun kawo muku cewa ma'aikatan gidan Zoo na jihar Kano sun bayyana cewa idan hanyoyin da ake bi na damke Zakin da ya kwace ranar Asabar ya gagara, za'a harbe dabban domin kare rayukan jama'a. Daily Nigerian ta ruwaito.

Zakin ya fasa cikin gidan Jimina kuma ya lashe daya kafin jami'an gidan suka turashi cikin kejin akuyoyi kuma hallaka biyu.

Diraktan gidan Zoo na Kano, Saidu Gwadabe, ya bayyanawa manema labarai a daren Lahadi cewa har yanzu ana cigaba da kokarin cewa na kama Zakin da ransa.

Gwadade yace kawo yanzu, Zakin ya kashe Jimina biyu da akuyoyi da dama: "Zakin ya kwace gidan Jiminan kuma ya cinye biyu,"

Asali: Legit.ng

Online view pixel