APC ta nada gwamnoni biyu daga arewa su jagoranci yakin neman zabe a Kogi da Bayelsa

APC ta nada gwamnoni biyu daga arewa su jagoranci yakin neman zabe a Kogi da Bayelsa

- Jam'iyyar APC ta rantsar da kwamitocin yakin neman zaben gwamna a jihohin Bayelsa da Kogi a zaben watan Nuwamba

- An nada gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'ai a matsayin jagoran yakin neman zaben jam'iyyar APC a jihar Kogi

- Gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar, jam'iyyar APC ta nada domin ya jagoranci yakin neman zaben APC a jihar Bayelsa

Jam'iyyar APC, mai mulki, ta rantsar da kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar a zaben gwamnan da za a yi a cikin watan Nuwamba a jihohin Kogi da Bayelsa.

A yayin da aka nada gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i a matsayin jagoran yakin neman zaben jam'iyyar APC a jihar Kogi, an rantsar da takwaransa na jihar Jigawa, Badar Abubakar, a matsayin wanda zai jagorancin yakin neman zaben jam'iyyar a jihar Bayelsa.

DUBA WANNAN: Daukaka kara: Jerin sunayen manyan alkalai 7 da PDP ke son a nada domin sauraron karar da Atiku da Buhari

Da yake magana a wurin rantsar da kwamitocin yakin neman zaben a hedikwatar jam'iyyar APC ta kasa, shugaban jam'iyyar, Adams Oshiomhole, ya bukaci kwamitocin su mayar da hankali wajen tabbatar da cewa jam'iyyar ta kai ga nasara a zabukan da za a yi a jihohin.

A ranar 16 ga watan Nuwamba ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta tsayar domin gudanar da zaben gwamna a jihohin Bayelsa da Kogi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel