Zaben Kogi: Ban marawa tazarcen Gwamna Bello baya ba – Dan takarar gwamna a PRP

Zaben Kogi: Ban marawa tazarcen Gwamna Bello baya ba – Dan takarar gwamna a PRP

- Dan takarar jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP) a zaben gwamna da za a yi a jihar Kogi ya nesanta kansa daga batun marawa tazarcen Gwamna Yahaya Bello baya

- Mista Ayodele Ajibola yace jam’iyyarsa ta shirya ma zaben gwamnan jihar mai zuwa kuma cewa ba za ta taba dinkewa da wani ba

- A cewarsa ya sha fama domin zama dan takarar daya daga cikin jam’iyyun siyasa mafi tsufa a Najeriya sannan kuma cewa ba zai taba siyar da cancantarsa don wani abu ba

Mista Ayodele Ajibola, dan takarar jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP) a zaben gwamna da za a yi a jihar Kogi ya nesanta kansa daga batun marawa tazarcen Gwamna Yahaya Bello na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) baya.

Ajibola ya bayyana hakan ne yayinda yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar, 19 ga watan Oktoba a Lokoja.

A cewarsa, jam’iyyarsa ta shirya ma zaben gwamnan jihar mai zuwa kuma cewa ba za ta taba dinkewa da wani ba.

KU KARANTA KUMA: Za a rantsar da sabon mataimakin gwamnan Kogi a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba

Dan takarar na jam’iyyar PRP yace ya sha fama domin zama dan takarar daya daga cikin jam’iyyun siyasa mafi tsufa a Najeriya sannan kuma cewa ba zai taba siyar da cancantarsa don wani abu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel