Sojoji sun kashe 'yan bindiga, sun kubutar da mutane uku a Kaduna

Sojoji sun kashe 'yan bindiga, sun kubutar da mutane uku a Kaduna

Dakarun rundunar sojojin Najeriya a karkashin atisayen 'Thunder Strike' sun kashe wasu 'uan bindiga da ake zargin suna sace mutane domin yin garkuwa da su a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Mataimakin darektan sashen hulda da jama'a na rundunar sojoji da ke Kaduna, Kanal Ezindu Idimah, shine wanda ya sanar da hakan a cikin sanarwar da ya fitar, inda ya ce dakarun soji sun kubutar da wasu mutane uku da 'yan bindigar suka sace a kauyen Maro ranar Laraba.

"Dakarun rundunar soji sun kai hari wata maboyar 'yan bindiga bayan samun bayanan sirri a kan cewa 'yan bindiga na rike da wasu jama'a da suka sace a wurin.

DUBA WANNAN: Badakala: EFCC ta gabatar da karin shaidu a kan wasu tsofin gwamnonin PDP biyu daga arewa

"An yi musayar wuta da 'yan bindigar kafin daga bisani a kashe daya daga cikinsu, ragowar kuma suka samu raunuka.

"Kwamandan rundunar soji da daya da ke Kaduna yana kira ga jama'a da su sanar da hukuma a duk inda suka ga wani da raunin harbin bindiga," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel