Kalli bidiyon yadda aka sanya wani barawo gyaran kwata bayan an kama shi yana sata

Kalli bidiyon yadda aka sanya wani barawo gyaran kwata bayan an kama shi yana sata

A yanzu haka abunda ke tashe a shafukan sadarwa shine wani bidiyo na wani barawo da aka tursasa shi gyara kwata bayan an kama shi yana sata a yankin Surulere, jihar Lagas.

Ga dukkan alamu an fara barin wannan mummunan dabi’a na daukar doka a hannu ta hanyar yiwa wadanda aka kama mummunan lahani daga kasahen Afrika da dama yayinda a yanzu mutane ke samo sabbin hanyar hukunta masu laifi da aka kama suna aikata barna.

Kwanan nan ne dai aka kama wani barawo a Surulere, Lagas sannan maimakon daukar doka ahannu ko mika shi ga yan sanda, sai aka sanya shi gyaran kwata a matsayin hukuncinsa.

Bidiyon wanda tuni ya shahara, ya nuna barawon na cire ciyayi daga kwatan wanda ke cike da ruwa.

KU KARANTA KUMA: Wata budurwa ta fadi aka rika yin zina da su a gidan 'azabtarwa' na Kaduna (Bidiyo)

Kalli bidiyon a kasa:

Wannan ba shine karo na farko da ake yiwa wanda aka kama yana sata irin wannan hukunci ba.

A cewar mai amfani da shafin Twitter wanda ya yada hotunan faruwar lamarin, yace an kama shi ne yana sata amma maimakon yi masa lahani ta hanyar daukar doka a hannu kamar yadda aka saba yi a Najeriya, sai aka sanya shi gyara masu kwata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel