Za a rantsar da sabon mataimakin gwamnan Kogi a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba

Za a rantsar da sabon mataimakin gwamnan Kogi a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba

An dage bikin rantsar da Edward Onoja a matsain sabon mataimakin gwamnan jihar Kogi zuwa ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba, wani rahoton jaridar The Nation ya yi ikirari.

Da farko an shirya gudanar da bikin rantsuwar ne a ranar Asabar, 19 ga watan Oktoba, biyo bayan tsige Simon Achuba a matsayin mataimakin Gwamna Yahaya Bello da majalisar dokokin jihar tayi.

Jaridar ta ruwaito cewa za a gudanar da bikin rantsarwar a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba lokacin da majalisar dokokin jihar za ta tantancee da tabbatar da Onoja a matsayin sabon mataimakin gwamnan.

Onoja, bayan tabbatarwar, zai koma gidan Lugard inda zai karbi rantsuwar aiki daga wajen babban shugaban alkalan jihar, Justis Nasir Ajanah.

Onoja ya kasance abokin takarar Gwamna Bello a zaben gwamnan jihar mai zuwa a ranar 16 ga watan Nuwamba.

Kafin zamantowarsa abokin takarar Bello, Onoja ya kasance shugaban ma'aikatan Bello.

KU KARANTA KUMA: Bita da kulli: Bayan tsige mataimakin gwamnan, jami'an tsaro sun zagaye gidansa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa mataimakin gwamnan jihar Kogi wanda majalisar dokokin jihar ta tsige, Mista Simon Achuba, ya bayyana cewa har yanzu shine mataimakin gwamnan jihar.

Achuba, wanda yayi magana ta hannun lauyansa, Mista Jibrin Okutepa (SAN), a wata hira da manema labarai yace ba a same shi da laifin ko daya daga cikin zarge-zargen da ake masa ba.

Yace zai kalubalanci tsigewar da aka yi masa a kotu, inda ya kara da cewa ba a cire shi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel