Daga karshe: Buhari ya yi magana a kan yaran da aka sace a Kano

Daga karshe: Buhari ya yi magana a kan yaran da aka sace a Kano

Shugaba Muhammadu Buhari ya yabawa Rundunar 'Yan Sandan Najeriya kan ceto yaran nan 9 da aka sace a Kano da kuma gano cibiyoyin gyaran tarbiyya na bogi a jihohin Kaduna da Katsina.

Shugaban kasar ta bakin babban mai taimaka masa na musamman kan kafafen watsa labarai, Garba Shehu, a Abuja a ranar Asabar ya bukaci 'yan sandan su cigaba da naminjin kokarin da suke yi a jihon kasar.

Da ya ke magana a kan mutanen da aka kama dangane da lamuran biyu, Shugaba Buhari ya ce kamen da aka yi ya yi dai-dai da tsarin gwamnatinsa na kiyaye hakokin dan adam da kima da darajar 'yan kasa ba tare da la'akari da shekaru, addini ko kabilunsu ba.

Ya ce ba zai amince da duk wani aikin barna ba da suka hada sa sace 'yara da kuma sayar da su.

DUBA WANNAN: Tirkashi: Ba don doka ba, da na bindige mahaifi na har lahira, inji jarumi Dabo

A kan batun gidajen gyaran tarbiya da ake azabtar da mutane kuma, shugaban ya ce babu wata gwamnatin demokradiyya mai hankali da za ta bari a kafa irin wuraren azabtarwa da sunan wurin gyaran hali.

Ya yabawa rundunar 'yan sanda saboda tona asirin masu kafa irin wannan cibiyoyin da mutanen da ke cin zarrafin al'umma.

Ya bayyana cewa gwamnati za ta cigaba da sa ido domin tabbatar da cewa an hana afkuwar irin hakan a gaba.

Shugaban kasar ya yi kira ga al'umma su cigaba da sa ido kuma su taimakawa hukumomin tsaro da bayyanai kan irin wannan laifin da ma sauran laifuka a unguwanninsu.

Ya ce, "Tsaro ya rataya a wuyan kowa idan har muna son mu tsaftace garuruwan mu kuma gwamnati a shirye ta ke ta tallafawa 'yan sanda ta hanyar samar musu da kudade da inganta walwalan ma'aikatansu domin su kara jajircewa wurin aiki."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel