Da dumi-dumi: Yan sanda sun ceto mutum 147 daga wata cibiyar horo a Kaduna

Da dumi-dumi: Yan sanda sun ceto mutum 147 daga wata cibiyar horo a Kaduna

- Yan sanda sun sake kai farmaki wata haramtacciyar cibiyar horar da kangararru a yankin Rigasa dake jihar Kaduna

- A wannan karon gwamna Nasir El-Rufai ya kasance tare da jami’an tsaron a lokacin da suka kai farmakin

- An ceto akalla mutane 147 tare da wasun su a daure

Rahotanni sun kawo cewa yan sanda sun sake kai farmaki wata haramtacciyar cibiyar horar da kangararru a yankin Rigasa dake jihar Kaduna.

An tattaro cewa a wannan karon, gwamna Nasir El-Rufai ya kasance tare da jami’an tsaron a lokacin da suka kai farmaki haramtacciyar cibiyar dake karamar hukumar Igabi a jihar.

An ceto akalla mutane 147 tare da wasun su a daure daga cibiyar wanda aka fi sani da cibiyar horar da kangararru na Malam Niga’.

Daga cikin wadanda aka ceto akwai mata 22 da yan kasar waje hudu yayinda jami’an tsaro suka tafi da mai cibiyar don gudanar da bincike.

KU KARANTA KUMA: An kama ‘yan KAROTA 3 dake sayar wa mutane da takardar daukan aiki ta jabu

Daga karashe dai an kai wadanda lamarin ya cika dasu zuwa sansanin yan Hajji a a yankin Mando dake Babban birnin jihar don samun cikakkiyar kulawa.

A cewar gwamnatin, za a sada su da iyalensu idan aka kammala basu kulawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel