Babachir Lawal yace Buhari zai fuskanci shanayensa a Daura bayan 2023

Babachir Lawal yace Buhari zai fuskanci shanayensa a Daura bayan 2023

- Babachir David, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi ritaya zuwa mahaifarsa, Daura, bayan ya bar mulki a 2023

- Lawal yace zai so ya ga Buhari ya bar tarihi mai cike da nasarori da dama bayan kammala mulkinsa

- Ya jaddada cewa shugaban kasar zai fuskanci shanayensa kamar yadda shima yake yi a yanzu

Tsohon babban sakataren gwamnatin tarayya, Babacir Lawal, ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi ritaya zuwa gida Daura domin kula da shanayensa bayan kammala mulkinsa a 2023.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Lawal ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana akan siyasa a Najeriya gabannin zaben 2023 tare da manema labarai a garin Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Dan siyasan yace zai so Buhari ya bar tarihi na fada idan lokacin barinsa mulki yayi.

KU KARANTA KUMA: Haramci: Kuma dai, Yan Shi’a na neman sulhu da gwamnatin tarayya

“A 2023 lokacin da mulkin Buhari zai kare, zai koma gida Daura domin fuskantar shanayensa kamar yadda nake yi. Amma kun gani, dole kowani shugaba ya bar abun fadi. Zan so naga ya bar tarihi mai cike da nasara,” inji Babachir.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Babachi Lawal, yace Bola Tinubu, babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na da kyakyawar damar zama Shugaban kasar Najeriya na gaba.

Yace Tinubu na da duk wasu nagarta da ake bukata daga Shugaban kasa na zamani domin maye gurbin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel