Haramci: Kuma dai, Yan Shi’a na neman sulhu da gwamnatin tarayya

Haramci: Kuma dai, Yan Shi’a na neman sulhu da gwamnatin tarayya

- Mambobin kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN) wacce aka fi sani da Shi'a sun karyata ikirarin cewa sun kasance rukunin Musulmai masu tayar da zaune tsaye

- Mambobin na IMN sun bayyana cewa babu wata hanya da za su bi su nuna bautarsu ga Allah da ya wuce yin tattaki a unguwanni cikin lumana

- Don ka kungiyar ta mika wata budaddiyar gayyata zuwa ga gwamnatin tarayya domin yin sulhu bayan an haramta ta

Haramtaciyyar kungiyar nan ta Islamic movement Of Nigeria (IMN), wacce aka fi sani da Shi’a a ranar Asabar a Katsina, ta gayyaci gwamnatin tarayya domin su tattauna tare da magance matsalolin da sauran abubuwa da suka kai ga haramta ta da gwamnatin tayi.

Shugaban yan uwa Musulmin a Katsina, Malam Yahaya Yakubu wanda ya kaddamar da hakan yayinda yake jawabi ga manema labarai daga cikin shirye-shiyensu na bikin Arbaeen, wanda suke tunawa da kisan Hussein, jika Annabi Muhammad, yace koda dai kungiyar ta daukaka kara akan haramcin sannan suna da tabbacin yin nasara akan gwamnati koda kuwa sau bakwai ne, a shirye suke su shiga tattaunawa da gamnatin domin magance dukka lamuran cikin lumana.

Yace: "kofarmu a bude suke a koda yaushe domin tattaunawa da gwamnatin tarayya, ba matsala bane bari gwamnati ta fahimce mu koda dai mun riga mun fahimce su, bamu da wata kasa sai Najeriya.

"Bamu da wata hanyar nuna bautarmu ga Allah sama da yin zanga zangar lumana a unguwanni sannan kuma bamu taba tayar da rikici ba, gwamnatin tarayya ta gabatar da hujjar da ke nuna cewa abunda muke yi ba daidai bane ko a wajen Allah idan har za su iya yin haka za mu daina."

KU KARANTA KUMA: Mutane 7 sun mutu bayan ayarin motocin Gwamna Obaseki sun yi hatsarin

Shugaban na Shi’a ya yi korafi akan rayukan da suka rasa a dukkanin lokutan da yan sanda ke farma mambobinsu idan suka fito yin tattaki inda yace a baya sun rasa akalla mutane a fadin jihohin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel