Pantami ya samu lambar yabo

Pantami ya samu lambar yabo

- Masana'antar sadarwa ta samu matukar cigaba a cikin kwanaki kalilan da Dr Pantami ya fara jagorantarta

- A cikin kwanakin ne aka rufe layikan wayoyi da ba a musu rijista yadda ya dace ba ko kuma basu da rijistar kwata-kwata kuma ana amfani dasu

- Ganin irin jajircewarsa da kwazon aikinsa ne yasa aka bashi lambar yabo ga ministan sadarwan

Sakamakon cigaban da aka samu cikin kwanaki 60 da zamansa ministan sadarwa na Najeriya, aka bashi lambar yabo.

A cikin kwanakin ne duk bangarorin dake karkashin ma'aikatar saddarwan suka fara aiki gadan-gadan.

Duk wasu layikan waya da ba a musu rijista yadda ya dace ba an rufesu.

KU KARANTA: Bita da kulli: Bayan tsige mataimakin gwamnan, jami'an tsaro sun zagaye gidansa

Masana'antu da dama dake karkashin ma'aikatar sun fara kama alkiblar da ta dace bayan shekarun da suka dauka tamkar basu da amfani.

Ana kuwa iya danganta hakan da jajircewa da kwazon mai girma ministan sadarwa, Dr Isa Ali Ibrahim Pantami, FNCS, FBCS, FIIM.

A don haka ne Centre for Cyber Awareness and Development, mashiryan Africa Digital Heroes Award ta ba jarumin jinjinarta ta 2019 shi kadai.

Ya cancanci jinjinar ne saboda jajircewarsa, gaskiya da rikon amanarsa.

Tunda ya fara aikin gwamnati ba a taba samunsa da nuna banbancin kabila, laifin rashawa ko makamancin hakan ba.

Halaye irin nagarta, kokarin gini akan gaskiya, aiki tukuru don jaddada yarda tare da amincin da ke tsakaninsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari su suka jawo masa jinjinar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel