An kama ‘yan KAROTA 3 dake sayar wa mutane da takardar daukan aiki ta jabu

An kama ‘yan KAROTA 3 dake sayar wa mutane da takardar daukan aiki ta jabu

Jami’an KAROTA uku sun gurfana a gaban Babbar kotun Kano da laifin sayar da takardar daukan aikin ta bogi. Ga sunayen jami’an da aka kama wadanda suka amsa laifinsu ba tare da gardama ba; Nazifi Ali Cigari, Abbas Tijjani da Ado Aminu.

Musa Isah shi ne wanda shigar da karar a gaban kotu ranar Alhamis 17 ga watan Oktoba, bayan ya samu tarin bayanai da shaidu daga hannun wani jami’in tsaron mai suna Ekene Ikpeama.

KU KARANTA:SGF, Ministan Abuja, Bindow, Ribadu da wasu mutum 35 za su sulhunta rikicin APC a Adamawa

Ikpeama ya ce mutanen uku dai sun kasance suna hada kai ne da wani Abdujalal Salisu wanda yake basu takardun bogi na ma’aikatar FIRS da KAROTA suna sayarwa mutane.

Ekene ya cigaba da cewa, bayan labarin wannan aikin yazo kunnensa sai ya hada tawagarsa ta bincike kana kuma suka bazama cikin aiki. A sakamakon hakan ne suka cafke Abduljalal inji shi.

Kamar yadda Ekene ya ba wakilin jaridar Daily Nigerian labari, ya ce, an samu Cigari a lokacin da aka kai samamen kamo wadannan mutanen amma da ya ga jami’an tsaro sai ya zuba a guje.

A lokacin da aka kai Abdujalal ofis domin yayi bayani, sai ya ce, yana sane da cewa takardun na jabu ne amma a haka ya sayarwa mutane har uku.

Sauran mutum ukun sun aminta da cewa lallai sun aikata wannan laifin sakamakon binciken da aka yin a ganin takardun FIRS da KAROTA a cikin motocinsu.

Alkalin kotun, Jastis Egwuati bayan ya saurari karar ya dage shari’ar zuwa ranar 7 ga watan Nuwamba, 2019. A ranar ne shari’ar za ta cigaba, inji alkalin.

https://dailynigerian.com/karota-officials-in-court-for-selling-fake-offers-of-employment/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel