Mutane 7 sun mutu bayan ayarin motocin Gwamna Obaseki sun yi hatsarin

Mutane 7 sun mutu bayan ayarin motocin Gwamna Obaseki sun yi hatsarin

Rahotanni sun kawo cewa an tabbatar da mutuwar mutane bakwai a ranar Asabar, 19 ga watan Oktoba, bayan afkuwar wani hatsari a kusa da kauyen Ehor a babbar hanyar Benin-Ekpo.

Wadanda lamarin ya cika dasu sun hada da magidanta biyar da yara biyu, lamarin ya auku ne yayin da motarsu kirar Audi 80 ta kara da wata mota kirar Toyota Hilux.

Mutanen da ke cikin motar Hilux din sun kasance jami’an gidan Gwamnatin jihar Edo.

An tattaro cewa suna a hanyarsu na zuwa Ekpoma, hedikwatan karamar hukumar Esan ta yamma a madadin yan rakiyan Gwamna Godwin Obaseki wanda zai halarci taron bikin kammala karatun dalibai na jami’ar Ambrose Ali dake Ekpoma.

Kwamandan hukumar kare afkuwar hatsarurruka (FRSC) sashin Edo, Mista Anthony Oko wanda ya tabbatar da lamarin yace yara biyun sun mutu ne a hanyar zuwa asibiti.

Oko yace dukkan fasinjojin motar Audin sun mutu yayinda direban motar Hilux din ya ji rauni.

Ya alakanta afkuwar hatsarin ga kubcewar da motar tayi daga hannun direban motar Audin.

Shugaban FRSC din yace direban motar ya shigi gargada kafin karawa da Hilux din.

KU KARANTA KUMA: Kuma dai: Yanzun nan yan sanda sun sake kai mamaya wani gidan Mari a Kaduna

Wani jami’in gwamnatin Edo wanda yayi magana ba tare da bayyana asalinsa ba yace jami’an basu ji rauni mai tsanani ba.

Kwamishinan yan sandan jihar, Danmallam Mohammed wanda ya tabbatar da lamarin ya bayyana shi a matsayin “abun bakin ciki”.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel