SGF, Ministan Abuja, Bindow, Ribadu da wasu mutum 35 za su sulhunta rikicin APC a Adamawa

SGF, Ministan Abuja, Bindow, Ribadu da wasu mutum 35 za su sulhunta rikicin APC a Adamawa

-An nada kwamitin sulhu domin ya dubu rikicin jam'iyyar APC a jihar Adamawa

-Boss Mustapha, Ministan Abuja, Nuhu Ribadu da Bindow Jibrilla duk suna cikin kwamitin mai kunshe da mutum 39

-Rikicin na APC a Adamawa ya samo asali ne a lokacin zaben gwamnan jihar da ya gabata

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Gida Mustapha da Ministan Abuja, Muhammad Bello su ne kan gaba a cikin wani kwamitin mutum 39 wanda zai sansanta rikicin da ya barke a cikin jam’iyyar APC reshen jihar Adamawa.

Tsohon gwamnan jihar Adamawa, Mohammed Bindow Jibrilla tare da abokin takararsa a zaben da ya gabata kuma tsohon shugaban hukumar EFCC, Mallam Nuhu Ribadu su na cikin wannan kwamitin.

KU KARANTA:Soke zaben June 12 zai cigaba da bibiyar mahaifina har iya tsawon rayuwarsa, inji babban dan IBB

Kwamitin gaba dayansa na mutum 39 da ne, inda Alhaji Abdulrahman Adamu zai kasance jagora wanda zai zanta da kwamitin zartarwa na APC a matakin kasa a kan abinda kwamitin nasa ya tattauna.

An dai samu rabuwar kawuna ne tsakanin jam’iyyar APC a zaben da ya gabata, inda wadansu ke tare da uwargidan Shugaban kasa dad an uwanta, wasu kuma na bangaren SGF na wancan lokacin Babachir Lawal, haka kuma Nuhu Ribadu da Gwamna Bindow kowa da na shi jama’ar.

Kamar yadda wani rahoton da ya samu kaiwa hannun ‘yan jarida ya fadi, an kafa wannan kwamitin ne domin dinke duk wata baraka da ta kunno kai a tsakanin ‘yan APC a Adamawa.

Haka zalika, ana sa ran kwamitin zai maido da kan ‘yan jam’iyyar a hade a matsayin tsintsiya madaurinki daya domin fuskantar jam’iyyun adawa a zaben dake tafe nan gaba.

https://thenationonlineng.net/sgf-fct-minister-ex-governor-ribadu-35-others-to-reconcile-adamawa-apc/amp/?__twitter_impression=true

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel