Kano: An kama buhunnan shinkafa 250 da aka boye cikin tankan man fetur (Hoto)

Kano: An kama buhunnan shinkafa 250 da aka boye cikin tankan man fetur (Hoto)

Hukumar Kwastam ta Najeriya reshen jihohin Kano/Jigawa a ranar Juma'a sun kama buhunnan shinkafan kasashen waje 250 da aka boye cikin wata tankar man fetur a kan hanyar Dura ziwa Kano da ya kamata a biya mata kudin haraji fiye na naira miliyan 5.5.

Shugaban rundunar, Nasir Ahmed ya ce wannan sabon dabarar shigo da kaya ta haramtaciyar hanya sabon lamari ne a yayin da ya ke nuna wa manema labarai shinkafar da aka kwace.

"Abinda muka gani a yau sabon lamari ne da ke caja mana kwakwalwa. Idan har mutum zai iya boye masara a cikin tankar dakon man fetur ko dizal ko kalanzir, muna ganin babu abinda ba za a iya boye wa a tankin ba.

Kano: An kama buhunnan shinkafa 250 da aka boye cikin tankan man fetur (Hoto)
Kano: An kama buhunnan shinkafa 250 da aka boye cikin tankan man fetur (Hoto)
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Tirkashi: Ba don doka ba, da na bindige mahaifi na har lahira, inji jarumi Dabo

Ya ce, "Ana iya dauka Tramadol ko bindigu da sauran makamai ko wani haramtaccen abu kuma sun tsara shi ta yadda zai yi wahala a gano.

"Amma saboda hikima da jajircewa wurin aiki na ma'aikatan mu, mun iya gano shi".

Mista Ahmed ya ce ajiye shinkafa ko wani abinda za a ci a irin wannan hali yana da matukar hadari da lafiyar mutane tare da lalata tattalin arziki da barazanar tsaro ga kasa.

Ya yi kira ga al'umma su rika tallafawa gwamnatin tarayya a yunkurin ta na hana fasakwabri su dena sayan kayayakin da aka shigo da su ta haramtattun hanyoyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel