Rufe boda: Kungiyar 'yan kasuwa a Ghana za su kauracewa kayan Najeriya

Rufe boda: Kungiyar 'yan kasuwa a Ghana za su kauracewa kayan Najeriya

Kungiyar 'Yan kasuwa na Ghana (GUTA) sun yi kira ga mambobinsu su kauracewa kayayyakin da ake shigarwa kasarsu duba da cewa rufe boda ta Najeriya ya jefa kasashen Afirka ta Yamma cikin mawuyacin hali.

'Yan kasuwan suna sa ran wannan matakin da suka dauka zai tilastawa gwamnatin Najeriya ta bude iyakokin ta na kasa domin a fara shigo da kayayyaki daga kasashen waje. Tun a watan Augusta ne Najeriya ta fara rufe wasu iyakokin na ta.

A cewar Ghanaweb.com, Sakataren GUTA na Greater Accra, David Kwadwo Amoateng a gidan rediyon Adom FM, Dwaso Nsem, a ranar Juma'a ya ce gwamnatin Najeriya ba ta yi wa 'yan kasuwan kasashen waje adalci ba. Yana kuma tsamanin gwamnatin Ghana za ta haramtawa 'yan kasuwar Najeriya da ke Ghana shigo da kayayaki amma hakan bai yi wu ba.

DUBA WANNAN: Tirkashi: Ba don doka ba, da na bindige mahaifi na har lahira, inji jarumi Dabo

Cikin fushi ya ce, "Ko dai an bawa wani 'na goro' ko kuma dai mu raggwaye ne. Gwamnati ba ta yi mana adalci ba.

Mista Amoateng ya bayar da misalin yadda Dangote ya mamaye kasuwani yayin da sauran 'yan kasuwa daga GHACEM suna shan bakar wahala.

Ya ce, "Ya kamata mu kauracewa kayayakin Najeriya don abinda gwamnatinsu tayi mana. Ta yaya za a mayar da mu bayi a kasar mu?".

Amoateng ya kara da cewa idan ba a dauki mataki kan lamarin ba akwai yiwuwar samun matsala wurin cinikayya a nahiyar.

Ma'aikatan harkokin kasashen waje na Ghana ta roki 'yan kasuwar Ghana su kara hakuri a yayin da ta ke tattaunawa da hukumomin Najeriya don ganin yadda za a bude iyakokin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel