A doke ka a hanaka kuka: Bayan taje Fasto ya dirka mata cikin shege, matar ta zo tana rokar mijinta ya kula da jaririn

A doke ka a hanaka kuka: Bayan taje Fasto ya dirka mata cikin shege, matar ta zo tana rokar mijinta ya kula da jaririn

- Wata matar aure ta shiga halin ha'ula'i bayan ta dauki cikin shege

- Matar wacce ba a bayyana sunanta ba Faston cocin su ya banka mata cikin shege bayan taki yadda ta kwanta da mijinta na tsawon watanni biyar

- Sai dai kuma yanzu matar ta zo tana rokar mijin nata da ya daure ya dauki nauyin jaririn da ta haifa

Wani labari na wani miji da mata mai ciki ya bazu a shafukan sada zumunta. Matar dai ta shiga wani mawuyacin hali bayan ta rasa yanda zata yi da cikin dake jikinta, bayan Fasto ya dirka mata ciki.

Kamar yadda aka ruwaito matar wacce ba a bayyana sunanta ba taje Faston cocinsu ya dirka mata cikin shege. Asirinta ya tonu ne kuma bayan ta shafe sama da wata biyar bata kwanta da mijinta ba, kawai sai gani aka yi ciki ya fito.

KU KARANTA: Bayan ta dauki kafa tun daga garinsu ta tafi wani gari domin ta hadu da saurayin da take Chatting da shi, a karshe ta gano cewa yarone dan shekara 12

Legit.ng ta samu wannan labari ne bayan wata mai amfani da shafin Twitter mai suna Miss Peter ta wallafa labarin a shafinta. Miss Peter ta bayyana cewa ma'auratan suna da dangantaka da ita.

Miss Peter ta bayyana cewa mijin ya bayyana cewa matar tashi ta shafe sama da watanni biyar ba ta kwanta da shi ba. Sai kuma yanzu ta zo tana rokon shi akan ya dauki nauyin jaririn da za ta haifa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel