Soke zaben June 12 zai cigaba da bibiyar mahaifina har iya tsawon rayuwarsa, inji babban dan IBB

Soke zaben June 12 zai cigaba da bibiyar mahaifina har iya tsawon rayuwarsa, inji babban dan IBB

Mohammed Babangida babban dan tsohon Shugaban Najeriya na mulkin soja wato IBB ya ce, mahaifinsa ya fada masa cewa soke zaben 12 ga watan Yuni, 1993 da yayi zai cigaba da bibiyarsa har tsawon rayuwarsa.

Soke wannan zaben ya jefa Najeriya da MKO Abiola cikin halin rudani da takaici. Abiola a wancan lokacin shi ne ya lashe zaben da aka gudanar. Daga bisani bayan soke zaben aka kulle shi a gidan yari inda ya mutu kafin a fito da shi.

KU KARANTA:‘Yan sandan Abuja sun cafke mutum 49 bisa zargin fashi da makami da kuma satar mutane

A cikin wata tattaunawa da jaridar The Sun babban yaron Babangida ya bada labarin abinda ya faru a daren ranar da aka yi zaben.

Mohammed ya ce: “Muna zaune ne a falon fadar Shugaban kasa wato Villa, sai mahaifinmu ya fito yake fada mana na soke zaben yau 12 ga watan Yuni. Dukkaninmu sai muka dubi juna cikin mamaki, muka ce da shi, meyasa kayi haka?

“Sai ya ce damu ku yara ne ba za ku fahimci dalilina na yin hakan ba a yanzu. Sai muka ce ko da yake wannan abu ne wanda ya shafi mulkinka da kuma gwamnatinka. Sai ya ce tabbas wannan abin zai cigaba da bibiyata har tsawon rayuwata.”

Mohammed ya cigaba da cewa, tuni ‘yan Najeriya suka mance da abinda ya faru bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya karrama Abiola da sanya ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimokuradiyyar kasar.

Haka zalika, soke wannan zaben yayi wa wasu ‘yan Kudu maso yammaci amfani inda yake cewa wannan shi ne ribar soke zaben da mutane ba su magana a kansa.

https://www.thecable.ng/ibbs-son-june-12-annulment-will-haunt-my-father-for-the-rest-of-his-life/amp

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel