‘Yan sandan Abuja sun cafke mutum 49 bisa zargin fashi da makami da kuma satar mutane

‘Yan sandan Abuja sun cafke mutum 49 bisa zargin fashi da makami da kuma satar mutane

Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja a ranar Juma’a 18 ga watan Oktoba ta damke mutane 49 inda ake zarginsu da hannu cikin aikata laifuka daban-daban.

Kwamishinan ‘yan sandan Abuja, CP Bala Ciroma ya bayyana kama mutanen a matsayin cigaba ta bangaren yinkurin da jami’ansa ke yin a gani sun kawar da miyagun laifuka.

KU KARANTA:Zaben Shugaban kasa: An cigaba da musayar yawu tsakanin APC da PDP kan karar da Atiku ya shigar Kotun koli

Kwamishinan ya ce, jami’ansa sun samu bindigogi guda 7, harsashi biyu, motoci guda 12, adda guda 16, layu da sauran nau’ukan muggan makamai iri daban-daban a tare da mutanen.

A cewar Ciroma daga cikin mutum 49 da aka kama, mutum 21 ‘yan fashi da makami ne, 14 kum masu satar mutane, 8 masu kwacen mota, 5 masu fataucin kwayoyi da kuma dan damfara mutum daya.

Ciroma ya sake cewa, atisayen da aka bude wanda ya kunshi jami’an ‘yan sanda da sauran jami’an hukumomin tsaro a Abuja ya na cigaba da haihuwar da mai ido, musamman a bangaren dakushe satar mutane a kauyuka.

Rahotannin da muka samu daga jaridar Leadership sun bayyana mana cewa, rundunar ‘yan sandan ta samu nasarar cafke mutum 10 da suke das a hannu cikin ayyukan satar mutane a Rubochi, Kuje, Kwali da Abaji, kuma a yanzu haka ana kan bincikensu.

Mutanen da aka kama sun hada da; Mohammed Umar, Mohammed Abdulsalam, Abdullahi Bashir, Abdulrazak Ibrahim, Ibrahim Dogosika da Idris Ori.

Sauran kuwa su ne, Friday Taye, Abdullahi Ibrahim, Garba Abubakar da Abdullahi Mohammed. Akwai kuma wani Saadu Abubakar da aka kama sakamakon binciken da ‘yan sanda suka yi bayan an sace wani mutum a Asokoro ranar 14 ga watan Satumba.

https://leadership.ng/2019/10/19/fct-police-parade-49-suspects-over-alleged-robbery-kidnapping/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel