Tinubu zai dace da zama Shugaban Najeriya na zamani – Babachir Lawal

Tinubu zai dace da zama Shugaban Najeriya na zamani – Babachir Lawal

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya wanda aka dakatar daga aiki, Babachi Lawal, yace Bola Tinubu, babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na da kyakyawar damar zama Shugaban kasar Najeriya na gaba.

Yace Tinubu na da duk wasu nagarta da ake bukata daga Shugaban kasa na zamani domin maye gurbin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.

Babachir, wanda ya bayyana hakan a Yola, jihar Adamawa, a wata hira da wasu zababbun manema labarai, ya kuma goyi bayan mika mulki ga yankin Kudu.

Yace a 2023, juya akalar mulki zai kasance daya daga cikin tarihin da shugaba Buhari zai bari a tsakanin wasu da dama.

Babachir, yayinda yake magana game da damar da kudu maso gabas ke dashi na samar da Shugaban kasa, ya yi watsi da cewar wani dan siyasar Igbo na da damar samun fifiko a daya daga cikin manyan jam’iyyun siyasar saboda har yanzu yan siyasa daga yankin basu kai ga cimma yarjejeniya ba.

KU KARANTA KUMA: Tsigewar da aka yi mun ba zai yi tasiri ba, har yanzu nine mataimakin gwamna – Achuba

Akan shugabancin Igbo, Babachir, yace a koda yaushe akwai wani ra’ayin cewa arewa na hana dan Igbo zama Shugaban kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel