Zaben Shugaban kasa: An cigaba da musayar yawu tsakanin APC da PDP kan karar da Atiku ya shigar Kotun koli

Zaben Shugaban kasa: An cigaba da musayar yawu tsakanin APC da PDP kan karar da Atiku ya shigar Kotun koli

Jam’iyyar APC mai mulkin a yanzu ta soki PDP a kan zarginta da tayi na neman cusawa Kotun koli wani ra’ayi na karon kanta dangane da shari’ar Shugaba Buhari da Atiku.

A ranar Alhamis 17 ga watan Oktoba, 2019 ne jiga-jigan PDP dake majalisar wakilai suka yi wata magana inda suke zargin APC da shirya munakisa a wurin Jastis Mohammed Tanko inda suke neman ya cire sunayen wasu alkalan da ya kamata a ce suna nan za a yi shari’ar.

KU KARANTA:Karyane masu satar mutane basu min fyade ba – Jaruma Maryam KK

‘Yan majalisar sun fadi cewa tun shekarar 1979 ana amfani ne da dadewar alkali a cikin ma’aikatar shari’a kafin a tura shi zuwa sauraron karar zaben shugaban kasa a kotun koli. A cewarsu ana son tursasa Jastis Tanko domin ya sauya wannan tsarin.

Jam’iyyar APC bata aminta da wannan zargin ba, inda ta fitar da martani a ranar Juma’a 18 ga watan Oktoba. Mai magana da yawun bakin jam’iyyar APC, Mallam Lanre Isa-Onilu ya ce wannan zargin na PDP maganar banza ce.

Onilu da yake zantawa da jaridar Tribune ya ce, babu wanda zai kama abinda PDP take fadi saboda jam’iyyace ita maras alkibla.

A cikin wani zance mai tsawon da kakakin Onilu ya fadi ya ce, abin takaici ne babu jam’iyyar hamayya a Najeriya. Kuma ya kara da cewa, kamata yayi a ce yanzu duk wani dan majalisa hankalinsa ya koma kan kasafin kudin 2020 amma ba maganar da bata da tushe ba.

Hon. Kingsley Chinda tare sauran ‘yan PDP dake majalisar ne suka fitar da wani zance, inda suke fadin cewa a shekaru 16 na mulkin PDP ba’a taba samun wani abu mai kama da wannan ba.

https://tribuneonlineng.com/atikus-appeal-apc-pdp-fight-over-supreme-court-justices/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel