Tsigewar da aka yi mun ba zai yi tasiri ba, har yanzu nine mataimakin gwamna – Achuba

Tsigewar da aka yi mun ba zai yi tasiri ba, har yanzu nine mataimakin gwamna – Achuba

Mataimakin gwamnan jihar Kogi wanda majalisar dokokin jihar ta tsige, Mista Simon Achuba, ya bayyana cewa har yanzu shine mataimakin gwamnan jihar.

Achuba, wanda yayi magana ta hannun lauyansa, Mista Jibrin Okutepa (SAN), a wata hira da manema labarai yace ba a same shi da laifin ko daya daga cikin zarge-zargen da ake masa ba.

Yace zai kalubalanci tsigewar da aka yi masa a kotu, inda ya kara da cewa ba a cire shi ba.

Okutepa yace: “Lamarin na a kotu. Sun yi watsi da lamarin a kotu. Lamain na nan zuwa. Za mu koma kotun. Najeriya kasa ce da ya kamata a dunga jagoranta da kundin tsarin mulki. Ba a kurmin daji muke ba.

“Babu wani tsigewa. Ba zai yiwu ka daura wani abu akan ba daidai ba sannan ka sa ran zai yi tasiri.”

KU KARATA KUMA: Bidiyo: Ta tabbata ya koma fim, an nuno sabon fim din da Sanata Dino Melaye ya fito a ciki

Shugaban kwamitin binciken zargin da ake yiwa Achuba, Mista John Baiyeshea (SAN), a wa hira da manema labarai yace kwamitin bata kama mataimakin gwamnan da lafin kowani zarfi da ake masa ba.

Ya bayyana cewa ba a tabbatar da zargin da ake yiwa mataimakin gwamnan ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel