Gwamnan Kogi ya maye gurbin mataimakinsa da aka tsige

Gwamnan Kogi ya maye gurbin mataimakinsa da aka tsige

Cikin kwanakin nan ne gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya zabi shugaban ma'aikatansa, Edward Onoja a matsayin mataimakinsa a takarar zaben 16 ga watan Nuwamba da ke tunkarowa a jihar.

Bello ya fito a matsayin dan takarar kujerar gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar APC a zaben fidda gwanin da aka yi a ranar 29 ga watan Augusta a Lokoja.

Gwamnan ya samu kuri'u 2,091 ne inda ya bige Babatunde Irukera da kuri'u 109.

A takarar da babban sakataren yada labarai na Gwamna Bello, Onogwu Muhammed ya bada a garin Lokoja, yace , shuwagabannin jam'iyyar APC ta kasa sun mika sunan Bello da Onoja ga INEC a matsayin masu neman kujerar gwamnan da mataimakinsa.

DUBA WANNAN: Tirkashi: Ba don doka ba, da na bindige mahaifi na har lahira, inji jarumi Dabo

Ya ce, zaben Onoja a matsayin mataimakin a wannan tafiyar ya biyo bayan tattaunawa da jin ra'ayoyin masu ruwa da tsaki a jihar.

Zaben Onoja a matsayin mataimaki a zabe mai gabatowa ba abin mamaki bane ga masana siyasa a jihar.

Onoja ya kasance tsohon abokin Gwamnan Bello kuma wani jigo a mulkin jihar karkashin Bello.

Ya taka rawar gani wajen habaka dokoki da manyan lamurran gwamnatin yanzu, zaben mutane da zasu cika guraben siyasa tare da saita gwamnatin Bello zuwa sabuwar alkibla.

Yayin bayyana amintakar da ke tsakaninsa da Onoja, Bello ba sau daya ba yake kiransa da "wanda aka haifesu manne".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel