Wani mutumi ya turawa babban amininshi 'yan daba su kashe shi, bayan ya ari naira dubu dari biyu ya kasa biyan shi

Wani mutumi ya turawa babban amininshi 'yan daba su kashe shi, bayan ya ari naira dubu dari biyu ya kasa biyan shi

- Wani mutumi mai suna Abolaji Kamaldeen ya nemi kashe babban abokin shi a jihar Legas

- An bayyana cewa mutumin ya nemi kashe abokin nashi ne ta hanyar aika masa da 'yan daba har gida sai dai mutumin ya gudu basu samu damar kashe shi ba

- An bayyana cewa mutumin ya tura a kashe shi dinne saboda ya karbi bashin kudi ya kasa biyan shi

Wani mutumi mai suna Abolaji Kamaldeen, wanda aka bayyana cewa ya ari naira dubu dari biyu a wajen babban abokinshi mai suna Ade Makanjuola, ya turawa abokin nashi 'yan daba su kashe saboda ya kasa biyan shi bashin.

Wannan lamarin dai ya faru a layin Ayanwale kusa da hanyar Ijegun dake yankin Ikotun cikin jihar Legas, a inda aminan suke zama.

An bayyana cewa wanda ake zargin, Kamaldeen yana fama da matsalar rashin kudi, kuma wata matsala ta taso masa wacce yake bukatar kudi, sai ya garzaya wajen abokin nashi, Makanjuola, ya ari wannan kudi da yarjejeniyar zai mayar masa zuwa wani lokaci.

Haka kuwa aka yi yayin da lokacin da Kamaldeen ya kamata ya biya shi kudin yayi bai biya ba, sai Makanjuola ya tunasar dashi maganar kudin.

KU KARANTA: Hotunan Bella Hadid: Mace Musulma da tafi kowacce mace kyau a duniya

Jami'an hukumar 'yan sanda sunyi zargin cewa akwai yiwuwar saboda Kamaldeen ya kasa biyan kudin ne yasa yaje ya debowa abokin nashi 'yan daba domin su kashe shi, amma kuma cikin ikon Allah Makanjuola ya samu ya kubuta.

Makanjuola ya kai karar wannan lamari zuwa wajen 'yan sanda, inda su kuma suka fara neman Kamaldeen suka kama shi.

Bayan an gabatar da bincike a kanshi, 'yan sandan sun same shi da laifi, inda suka mika shi kotu domin yanke masa hukunci akan laifukan da ya aikata, na kin biyan bashi da kuma dauko 'yan daba su kashe abokin shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel