Karyane masu satar mutane basu min fyade ba – Jaruma Maryam KK

Karyane masu satar mutane basu min fyade ba – Jaruma Maryam KK

-Jaruma Maryam KK ta karyata labarin da ake bayarwa a kan cewa masu satar mutane sun yi mata fyade

-Maryam ta ce abinda kawai aka yi mata lokacin da take tsaren shi ne dan banzan duka amma ba fyade ba

-A cikin watan Agustan 2019 ne wasu mutane suka sace jarumar inda suka sakota baya an biya N2m kudin fansa

Sabuwar jarumar nan wadda tauraruwarta ke haskawa a Kannywood wato Maryam KK ta fito domin karyata jita-jitar da ake yadawa cewa wai masu satar mutane sunyi mata fyade a watan Agustan 2019.

Jarumar ta bada labarin cewa, ko da yake dai ta ci bakar wuya a hannun barayin tare da mugunta irin daban-daban, amma ta karyata maganar cewa an yi mata fyade.

KU KARANTA:Gwamnatin tarayya da kasar Rasha za su hada hannu domin tayar da kamfanin karfen Ajaokuta – Minista

Jarumar ta sanar da mujallar karshen mako cewa, na kwana biyu kawai suka tsareta kuma suka saketa bayan an biya naira miliyan 2 a matsayin fansa.

Maryam ta ce: “Bayan anyi hakan sai aka kai ni ofishin ‘yan sanda da kuma banki domin na kulle asusun ajiyata. Daga baya kuma aka wuce dani zuwa asibiti inda aka duba lafiyata. Bayan na dawo cikin hayyacina ne nake yita jin labarai iri daban-daban.

“Wasu na cewa, wai ni da kaina na shirya a sace domin na samu kudi, inda wasu kuma ke fadin wai barayin sun yi mani fyade. Labarai dai iri daban-daban na yita ji. Abinda kawai na san anyi mani shi ne dukan tsiya da kuma bani gwale-gwale.” Inji jarumar.

Har ila yau, jarumar ta ce, har yanzu fargaba da tsoron wannan abin da ya faru da ita bai fita a ranta ba. Inda ta kara da cewa sai an dau tsawon lokaci kafin ta iya mantawa da wannan mummunan al’amarin da ya faru da ita.

https://www.dailytrust.com.ng/kannywood-actress-maryam-kk-denies-being-raped-by-abductors.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel