Karancin albashi: Ma'aikatar kwadago ta sanar da lokacin da za a fara biya

Karancin albashi: Ma'aikatar kwadago ta sanar da lokacin da za a fara biya

- Ministan kwadago, Chris Ngige ya bayyana cewa, fara biyan karancin albashin zai fara nan take ne

- Bayan taron kwanaki uku da kungiyar kwadago suka yi da wakilan gwamnatin tarayya, an samu matsaya

- Karin albashin ya dogara ne da tsarin albashin ma'aikaci da kuma matakin ma'aikacin

Ministan kwadago, Chris Ngige yace za a fara biya mafi karancin albashin ne a take kuma zai zagaya ne duk masana'antun gwamnati da masu zaman kansu.

Ya bayyana hakan ne jiya a Abuja, jim kadan bayan kungiyar da gwamnati ta wakilta ta gama taro da kungiyar kwadago.

KU KARANTA: Ministan Buhari ya nemi taimako daga Bollywood

Dama rashin daidaituwar da aka samu ya danganta ne da gyaran albashin ma'aikatan da tun farko sun wuce karancin albashin.

A bayanin da yayi bayan taron kwana ukun, Ngige ya bayyana gyaran albashin kamar yadda kungiyar kwadago ta aminta dashi kamar haka:

"Albashin ma'aikaci mai mataki na 7 a tsarin COMESS zai karu da 23%, mataki na 8 zai karu da 20%, mataki na 9 zai karu da 19%, mataki na 10 zuwa 14 zasu karu da 16% inda mataki na 15 zuwa 17 zasu karu da 14%,"

"Albashin ma'aikata masu tsarin albashi na CONHES, CONRRISE, CONTISS da sauransu karinsu shine: Mataki na 7 zasu samu karin 22.2%, mataki na 8 zuwa 14 zasu samu karin 16%, mataki na 15 zuwa 17 zasu samu karin 10.5%"

Ya ce kashi na uku a yarjejeniyar ta fada kan karancin albashin jami'an tsaro. Za a bayyana yanayin tsarin karancin albashinsu ta kafar da ta dace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
NLC
Online view pixel