Gwamnatin tarayya da kasar Rasha za su hada hannu domin tayar da kamfanin karfen Ajaokuta – Minista

Gwamnatin tarayya da kasar Rasha za su hada hannu domin tayar da kamfanin karfen Ajaokuta – Minista

Gwamnatin Najeriya ta ce tana kulla wani shirin hadin gwiwa da gwamnatin kasar Rasha domin farfado da kamfanin karfen Ajaokuta.

Ministan cigaban ma’adanan kasa, Mr Olamilekan Adegbite ne ya fadi wannan maganar a wata tattaunawa da yayi da kwamitin cigaban ma’adanan kasa na Majalisar dattawa ranar Juma’a 18 ga watan Oktoba a Abuja.

KU KARANTA:N10bn kudin gyaran filin jirgin Enugu: Majalisar wakilai ta yabawa Buhari

Ya kuma kara da cewa, daya daga cikin muhimman abubuwan da za su kai Shugaba Buhari kasar Rasha a mako mai zuwa shi ne maganar farfado da wannan kamfanin.

A cewarsa, kasar Rasha ta bayyana aniyarta na son taimakon Najeriya domin ta farfado da kamfanin karfen ta hanyar yin amfani da kudinta.

Adegbite ya ce: “Suna son ganin kamfanin karfen Ajaokuta ya tashi ya cigaba da aiki, wannan dalilin ne ya sanya muke kokari sanya su ciki aikin tare da ba su damar yin wadansu abubuwa.

“Aikin a halin yanzu ya kusa kammala, akwai kudaden da suka kawo domin a karkare aikin ta yadda idan an gama za suyi amfani da kamfanin domin neman riba, kana kuma daga bisani idan sun samu sai su mikawa Najeriya kamfaninta.

“A ganina wannan ita ce hanya mafi sauki da za a iya samun damar farfado da wannan kamfanin na Ajaokuta. Nan bada jimawa ba hakarmu za ta cinma ruwa game da aikin.” Inji shi.

A nasa jawabin kuwa, shugaban kwamitin cigaban ma’adanan kasa na majalisar dattawa, Sanata Tanko Almakura ya ce, akwai bukatar a gargadi jihohi da kananan hukumomi kan cewa su guji haramtacciyar hanyar hakan ma’adanan.

https://www.dailytrust.com.ng/fg-russian-government-to-partner-in-reviving-ajaokuta-coy-minister.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel