Bita da kulli: Bayan tsige mataimakin gwamnan, jami'an tsaro sun zagaye gidansa

Bita da kulli: Bayan tsige mataimakin gwamnan, jami'an tsaro sun zagaye gidansa

- An gano cewa, jami'an tsaro sun mamaye harabar gidan mataimakin gwamnan jihar Kogi da majalisar jihar ta tsige a ranar Juma'a

- Hakan kuwa ya jawo firgici da tashin hankali ga mazauna yankin doomin kuwa jami'an tsaron suna haramta shige da fice a gidan tsohon gwamnan

- Tsohon mataimakin gwamnan ya kwatanta abinda majalisar tayi da 'mara amfani' kuma barazana ga damokaradiyya

An gano cewa, jami'an tsaro masu tarin yawa sun zagaye gidan Simon Achuba, tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi da majalisar ta tuge a ranar Juma'a.

Jami'an tsaron sun hana shige da fice a gidan. Hakan kuwa ya kawo firgici da tashin hankali ga jama'ar yankin.

KU KARANTA: Toh fah: IGP ya gayyaci dan takarar gwamnan jihar Zamfara

Majalisar jihar Kogi ta tsige mataimakin gwamnan ne a ranar juma'a bayan da ta zarge shi da dabi'un da bata yarda dasu ba.

Achuba, ya tabbatar da hakan ne a daren Juma'a lokacin da aka nuna shi a wani shirin gidan talabijin na AIT a wani shiri na 'Damokaradiyyarmu a yau'.

Ya ce, "A halin yanzu da muke magana, jami'an tsaro na zagaye da gidana. Hadimina na tsaro an janye shi. A halin yanzu jami'an tsaron gidan gwamnati sun mamaye gidana. Babu mai shiga da fita daga gidana."

Amma kuma, Achuba ya kwatanta tsigeshin a matsayin mataimakin gwamnan jihar da abu mara amfani.

Kamar yadda ya sanar, Najeriya kasa ce da take mulkin damokaradiyya. Abinda majalisar jihar Kogi ta kwatanta kuwa barazana ce ga damokaradiyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel