An nada El-Rufa'i shugaban kamfen APC na zaben jihar Kogi, Badaru na Bayelsa

An nada El-Rufa'i shugaban kamfen APC na zaben jihar Kogi, Badaru na Bayelsa

- An sanar da masu ruwa da tsakin jam'iyyar All Progressives Congress APC da zasu jagoranci yakin neman zaben gwamna a jihar Kogi da Bayelsa

- Shugaban Jam'iyyar, Adams Oshiomole, ya bayyana hakan ranar Juma'a, 18 ga wa Oktoba, a Abuja

- A cewar Oshiomole, mambobin sun kunsi gwamnoni, tsaffin ministoci da masu ci, sanatoci da mambobin majalisar wakilai

An nada gwamna jihar Kaduna,Nasir El-Rufa'i, a matsayin shugaban kwamitin kamfen jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na zaben jihar Kogi ranar 16 ga Oktoba, 2019.

Hakazalika an nada gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru, matsayin shugaba kwamitin zaben gwamnan jihar Bayelsa da za'a gudanar rana daya da na Kogi.

SHIN KA SAN Hajiya Sadiya Umar Farouq ta kai ziyara inda akayi gobara a Onitsha (Hotuna)

An rantsar da kwamitin ne ranar Juma'a a sakatariyar jam'iyyar APC ta kasa dage unguwar Wuse2 Abuja.

Gwamna El-Rufa'i a jawabinsa ya ce kwamitinsa zata tabbatar da nasara a jihar Kogi kuma za tayi iyakan kokarinta wajen yiwa jam'iyyar adawa ta PDP birnewar karshe a jihar.

Yace: "Bayan kaddamar da kamfe, ina kira da dukkan mambobin kwamitin kamfen su koma Lokoja gaba daya domin shirin birne jam'iyyar PDP a jihar gaba daya,"

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, wanda yake mamban kwamitin Bayelsa yayi magana a madadin gwamna Badaru, ya bayyana cewa jam'iyyar za ta kwace jihar Bayelsa a zaben bana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel