Kotu ta dakatar da diban ma'aikata da NNPC ke yi

Kotu ta dakatar da diban ma'aikata da NNPC ke yi

- Babbar kotun tarayya dake Abuja ta dakatar da matatar man fetur ta kasa, wato NNPC daukar ma'aikata

- Hakan ya biyo bayan maka kotun da wani lauye mai kare hakkin bi adama yayi a gaban kuliya

- Lauyan ya kalubalanci matatar da tasa banbancin shekaru suka zamo shinge ga dubban 'yan Najeriya masu bukatar aikin

Babbar kotun tarayya dake Abuja ta bada umarnin dakatawa a daukar ma'aikata da matatar man fetur ta kasa keyi har zuwa lokacin da za a kammala sauraron karar da Pelumi Olajengbesi.

Olajenbesi, lauya mai kare hakkin mutane, ya bukaci a soke dibar aikin da matatar man fetur ta kas ke yi saboda a kare hakkin duk wadanda suka nemi aikin.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Hukumar EFCC ta cafke tsohon gwamnan jihar Zamfara

Dokar neman aikin ta haramtawa 'yan Najeriya masu shekaru 28 a duniya mika bukatar neman aikin dukm da kuwa akwai guraben.

Olajengbesi ya ga laifin dokar da ta sa shekaru su zam shinge tsakanin 'yan kasar da aikin ganin cewa da hakan yaci karo da sashi na 3(e)(iv) na hakkokin dan adam na shekara 2019 wanda aka yi don kare ra'ayin dan Najeriya.

Ya rubuta wasika ga babban manajan matatar, Dr Maikanti Baru, a ranar 26 ga watan Maris tare da barazanar zai maka matatar gaban kuliya akan 'yan Nageriya da aka musu katanga da aikin saboda banbancin shekaru.

A sauraron kara da kotu tayi a ranar 18 ga watan Oktoba, 2019, mai karar ya roki kotu da tayi adalci ga miliyoyin 'yan Najeriya da ke fama da rashin aikin yi.

"Ina rokon kotu da ta saurari shari'ar tare da suka ta farko da wadanda aake kara suka shigar a ranar 15 ga watan Oktoba," in ji wadanda ake kara.

Lokacin da aka kira shari'ar a ranar 15 ga watan Oktoba, lauyan mai kara ya bayyanawa kotu cewa, mai bashi da lafiya ahalin yanzu don anyi mishi aiki.

Alkalin kotun, Jastis Muhammed Tsoho na babbar kotu tarayyar ya sanar da lauyan wadanda ake kara cewa, sukar da aka shigar bata karbu ba.

A don haka ne Tsoho ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 29 ga watan Oktoba tare da umarnin dakatar da daukan ma'aikatan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel