Yanzu-yanzu: An dakatar da sakataren jam'iyyar APC a Jihar Edo

Yanzu-yanzu: An dakatar da sakataren jam'iyyar APC a Jihar Edo

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Edo ta dakatar da sakatarenta, Mista Lawrence Okah.

An dakatar da Okah ne yayin wata taron gaggawa da kwamitin masu rike da mukami na jam'iyyar suka kira.

Shugaban jam'iyyar na jihar, Barrista Ansle, Ojezua ya ce an dakatar da Okah ne a bawa kwamitin da aka kafa domin yin bincike a kansa damar yin bincikenta ba tare da katsalandan ba.

Ya ce, "An dakatar da shi ne domin kwamitin da gudanar da binciken da ta ke yi a kansa. Ba mu kore shi ba. Dakatarwar ba hukunci bane dama haka ake yi idan za a gudanar da bincike."

DUBA WANNAN: Hotunan gangariyan sabbin jiragen kasa na zamani da China ta kera wa Najeriya

A baya, Ojezua ya ce ba zai bari wata kungiya a cikin jam'iyyar ta APC na jihar ta raba kan jam'iyyar ba domin irin wannan kungiyoyin kamar cutar kansa suke.

Ya ce, "Duk wanda ya ke tunanin zai kafa wata kungiya ya ware kansa zai gamu da mu. Babu wata hanyar kashe jam'iyya da ya wuce raba kan 'yan jam'iyyar. Ba za mu raga wa duk wanda ya yi yunkurin hakan ba koma dokar jam'iyya ta yi bayani karara a kan hakan."

Gwamnan jihar, Godwin Obaseki ya ce zai fattaki dukkan wadanda ya ke ganin za su raba kan jam'iyyar.

A jawabin da ya yi yayin kaddamar da Edo Development and Property Authority, Obaseki ya yabawa 'yan jam'iyyar da suke yi wa jam'iyya biyaya amma ya sha alwashin korar wadanda ke neman raba kan jam'iyyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel