Toh fah: IGP ya gayyaci dan takarar gwamnan jihar Zamfara

Toh fah: IGP ya gayyaci dan takarar gwamnan jihar Zamfara

- Sifeta janar din 'yan sanda, Muhammed Adamu ya gayyaci tsohon dan takarar gwamnan jihar Zamfara don tattaunawa

- An bukaci ganin Sani Abdullahi Shinkafi ne a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba

- Ana zarginsa da bata sunan Magajin Garin Sokoto ne akan Halal Otal na Zamfara dake Abuja

Sifeta janar din 'yan sandan Najeriya, Muhammed Adamu, ya gayyaci dan takarar gwamnan jihar Zamfara karkashin jam'iyyar APGA a zaben 2019, Sani Abdullahi Shinkafi (Wamban Shinkafi) akan zarginsa da ake da bata sunan Magajin Garin Sokoto, Alhaji Hassan Ahmad Danbaba.

A wasikar gayyatarsa mai kwanan wata 16 ga watan Oktoba, 2019 da jaridar Solacebase ta gani, shugaban sashen kula sifeta janar din na hedkwatar 'yan sandan dake Abuja, mataimakin kwamishinan 'yan sanda A. A. Elleman ne yasa hannu.

Kamar yadda aka rubuta a wasikar, Shinkafi, wanda shine shugaban kwamitin karbo kadarorin gwamnatin jihar, an bukaci ganinsa ne a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba, 2019 da karfe 10 na safe.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Hukumar EFCC ta cafke tsohon gwamnan jihar Zamfara

Wasikar tana kunshe da kalamai kamar haka: "Ofishin binciken laifukan da suka hada da bata suna da kuma wallafa kalamai karya wadanda zasu iya kawo damuwa ga mutane, ya kawo rahoto ga sifeta janar din 'yan sanda kuma sunanka na ciki,"

"A saboda wannan dalilin ne, muke bukatar tattaunawa da kai ta wurin SP Usman Garba a ranar 21 ga watan Oktoba, 2019 da karfe 10 na safe don karin haske akan zargin da ake maka."

"Hadin kanka na da matukar amfani kuma zamuyi farinciki dashi."

A ranar 30 ga watan Satumba, 2019, Sani Abdullahi Shinkafi, ya rubuta budaddiyar wasika tare da ikirarin cewa, Magajin Garin Sokoto ya maida Otal din Halal na Zamfara dake Abuja zuwa amfanin kansa.

Hakazalika, ya zargi tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari da "damfara" wajen mikawa Alhaji Hassan Danbaba kadarori tare da ikirarin cewa otal din ya samar da naira miliyan dubu dari tara da hamsin a cikin shekaru takwas amma ko sisi bata shiga asusun gwamnatin jihar Zamfara ba.

Amma kuma, Magajin Garin Sokoto ya musanta zargin.

A don haka ne Alhaji Hassan Ahmad Danbaba ya shigar da karar Sani Abdullahi Shinkafi akan bacin suna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel