An kama wani fitinannen mai kashe mutane da abokin ta’asarsa a Osun

An kama wani fitinannen mai kashe mutane da abokin ta’asarsa a Osun

Rundunar yan sandan Osun ta kama wani mai suna Teslim Raji, wanda aka fi sani da Akerele, da wani abokin rakiyansa, Femi Bamidele, kan zargin yawan kashe-kashe, garkuwa da mutane da harbi a guje a yankin Ikire dake jihar.

Kwamishinan yan sandan jihar, Misis Abiodun Ige, yayinda take gurfanar da masu laifin a Osogbo, tace an kama ainahin babban mai laifin Raji, bayan wasu korafe-korafe da mazauna yankin suka kai.

Tace Raji, an kama Raji wanda ake bincike a shekarar da ya gabata, sannan aka kaishi kotu inda aka bayar da belinsa amma daga baya ya tsallake belin.

Tace bayan tsallake belin, sai mai laifin ya kama zuwa ya kashe wani sannan tun lokacin, yan sanda ke bibiyarsa.

KU KARANTA KUMA: Innaillahi wa’inna illahi raji’un: Bam ya halaka mutane 62 a masallacin Juma’a a Afghanistan

“An kama mataimakin nasa da fari lokacin da jami’inmu ya je gidansa sannan daya daga cikin yaransa yayi kokarin guduwa,” inji ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel