Kotun daukaka kara ta tabbatar na nasarar mijin shugabar kotun ta kasa

Kotun daukaka kara ta tabbatar na nasarar mijin shugabar kotun ta kasa

- Kotun daukaka kara reshen jihar Jos ta yi watsi da daukaka karar jam'iyyar NNPP da dan takararta

- Jam'iyyar NNPP na kalubalantar nasarar Sanata Bulkachuwa ne a zaben sanatocin da INEC ta bayyana ya lashe

- Jastis Tani ta yanke hukuncin cewa, kotun sauraron kararrakin zaben tayi daidai da tayi watsi da karar kuma kotun daukaka karar ma tayi hakan akan rashin kwararan shaidu

Kotun daukaka kara reshen jihar Jos, ta jaddada hukuncin kotun kararrakin zaben ta jiha da kuma kasa da ke Bauchi a ranar Juma'a.

Hakan ne kuwa ya kara yin watsi da karar da jam'iyyar NNPP da dan takararta Farouk Mustapha akan nasarar Adamu Bulkachuwa na jam'iyyar APC.

Mustapha ya mika karar ne me kalubalantar nasarar Bulkachuwa a dalilin karantsaye ga dokokin zabe da ake zarginsa.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Hukumar EFCC ta cafke tsohon gwamnan jihar Zamfara

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Bulkachuwa maigidan shugabar alkalan kotun daukaka kara ne, Zainab Bulkachuwa.

A ittifakin da kotun tayi wajen yanke hukuncin da Jastis Tani Hassan tayi, tace zargin rashin bin ka'idojin zabe a akwatuna 1,419 na mazabar da mai kara yayi, ya kasa bawa kotun sauraron kararrakin zaben da kuma kotun daukaka karar kwararan shaidu.

Kamar yadda alkalin ta sanar, tun a kotun sauraron kararrakin zaben, masu karar sun bada shaidu biyar ne kacal kuma takardun da suka bada na shaida babu gamsarwa.

"Take ka'idojin zabe ana iya ganesu ne ta hanyar bada shaidu a rubuce kuma kotun sauraron kararrakin zaben tayi daidai da bata dubi wannan wadannan takardun marasa gamsarwa," ta yanke.

Jastis Tani ta ce, shaida ta biyar da masu kara suka gabatar, yakamata ya zamo kwararre a bayanin MM da MN, amma ya sanar da kotun sauraron kararrakin zaben cewa shi ba kwararre bane.

Kamar yadda tace, kotun sauraron kararrakin zaben ta yi daidai da tayi watsi da karar.

"Ban ga amfanin daukaka karar ba, a don haka ne muka yi watsi da karar," ta yanke hukunci.

Jastis Tani ta kara bayyanawa cewa, nasarar Sanata Bulkachuwa da INEC ta sanar na nan daram.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel