Zaben gwamnan Kogi: Jam’iyyu 13 sun marawa Aisha Audu baya

Zaben gwamnan Kogi: Jam’iyyu 13 sun marawa Aisha Audu baya

Wasu jam’iyyun siyasa guda 13 sun yanke shawara marawa Farfesa Aisha Audu ta jam’iyyar Young Progressive Party (YPP) baya a matsayin yar takararsu a zaben gwamnan jihar Kogi da za a gudanar a ranar 16 ga watan Nuwamba.

Kakakin kungiyar, Mista Abdulkadir Adebayo ya bayyana hakan yayinda yake jawabi gamanema labarai a Abuja, a ranar Juma’a. 18 ga watan Oktoba jim kadan bayan sun shiga yarjejeniyar fahimta da yar takarar YPP.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa Aisha ta kasance uwargidar marigayi Prince Abubakar Audu, tsohon gwamnan jihar.

Adebayo ya koka kan wahala da matsin tattalin arziki da mutanen jihar ke fuskanta.

Ya bayyana cewa halin da mutanen jihar ke ciki bai yi daidai da tafarkin da tsohon gwamnan ke kai ba, wanda ya sha gwagwarmaya da yaki akai har ya mutu kan haka.

Adebayo ya bayyana cewa sun yanke shawarar marawa yar takarar YPP baya ne domin taimakamata wajen cimma mafarkin marigayin mijinta.

KU KARANTA KUMA: Innaillahi wa’inna illahi raji’un: Bam ya halaka mutane 62 a masallacin Juma’a a Afghanistan

A cewarsa, suna son yantar da mutanen jihar Kogi daga halin da suke ciki.

Yayinda take martani kan lamain, Misis Audu ta mayar da hankali kan bukatar samun yanci cikin lumana kuma sake gina jahar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel