Magidancin da ya yiwa ya shekara 9 fyade a Adamawa ya nemi ayi mai afuwa domin yace bai kammala ba aka kama shi

Magidancin da ya yiwa ya shekara 9 fyade a Adamawa ya nemi ayi mai afuwa domin yace bai kammala ba aka kama shi

Wani mai siyar da ruwa dan shekara 30 da aka kama yana lalata yarinya yar shekara tara a Adamawa ya roki da ayi mai rangwame kan hujjar cewa “bai kammala” ta’asar ba kafin aka kama shi.

Mai laifin, Mohammed Babangida, wanda hukumar tsaro na NSCDC ta gurfanar a ranar Juma’a, 18 ga watan Oktoba, ya fada ma manema labarai cewa shi sabon shiga ne a wajen aikata laifin, sannan cewa yayi danasanin abunda ya aikata.

“Wannan shine karo na farko da na aikata hakan sannan banma kammala ba lokacin da aka kwankwasa kofana, inda hakan ya tursasa ni dakatawa.

“Ina roko da a yafe mun a matsayina na magidanci dake da yara. Ina zama a Bauchi; bana son wannan abun kunyan ya wargaza iyalina.

KU KARANTA KUMA: An gurfanar da wani dan shekara 60 bayan ya yaudari wata bazawara da alkawarin aure

“Gaba daya abun ya fara ne wasu yan kwanaki da suka gabata lokacin da yarinyar ta roke ni N50 domin ta siya cincin, inda tayi ikirarin cewa tana jin yunwa, sai na bata.

“Sai ya kara dawowa ta roke ni kudi a wata rana san na bata N20; sai ta sake zuwa gidana na bata N50 sannan muka shiga daki,” inji Babangida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel