Miyagun da suka sace yaran Kano guda 9 ba Kiristoci bane – kungiyar CAN

Miyagun da suka sace yaran Kano guda 9 ba Kiristoci bane – kungiyar CAN

Kungiyar kiristocin Najeriya reshen jahar Kano ta nesanta kanta daga miyagun mutanen da suka sace kananan yara guda 9 a jahar Kano, suka kai su jahar Anambra, suka canza musu suna sa’annan suka sauya musu addini daga Musulunci zuwa Kiristanci.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito shugaban CAN na Kano, Adeyemo Samuel ne ya bayyana haka a ranar Juma’a, 18 ga watan Oktoba cikin wata sanarwa daya fitar dake dauke da sa hannunsa, inda yace sun barranta da mutanen.

KU KARANTA: Boko Haram: Dakarun Sojin Najeriya sun cigaba da samun narasa a kan yan ta’adda

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban na CAN yana cewa bai kamata a dinga danganta mutanen da kungiyar CAN ba saboda kungiyar bata taba goyon bayan irin wannan mummunan hali ba, haka zalika laifin da suka tafka bashi da alaka da koyarwar addinin kiristanci.

“Muna fayyace ma jama’a cewa CAN bata san wadannan miyagu ba, kuma basu da wata alaka da CAN, mutane ne kawai masu mummunar manufa sun kulla alaka da shaidan, don haka muke kira ga hukumomin tsaro su gudanar da bincike yadda ya kamata a kansu tare da gurfanar dasu gaban kotu domin su fuskanci hukuncin abinda suka aikata tare da duk masu hannu cikin laifin.” Inji shi.

Bugu da kari, Samuel ya yi kira ga al’ummar jahar Kano da kada su bari wannan lamari ya kawo tsatstsamar dangantaka tsakanin mabiya addinin Musulunci da Kiristoci, sa’annan ya yaba ma rundunar Yansandan Kano bisa kokarin da ta yi.

Daga karshe shugaban ya jinjina ma gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje sakamakon kokarin da yake wajen tabbatar da zaman lafiya a jahar, kamar yadda bayyana jin dadinsu game da rawar da Sarkin Kano yake takawa wajen hadin kan al’ummar Kano.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel