N10bn kudin gyaran filin jirgin Enugu: Majalisar wakilai ta yabawa Buhari

N10bn kudin gyaran filin jirgin Enugu: Majalisar wakilai ta yabawa Buhari

Kwamitin majalisar wakilai wanda ke kula da sufurin jiragen sama, ya yabawa Shugaba Muhammadu Buhari a kan naira biliyan 10 da ya bada domin gyaran filin jirgin saman Akanu Ibiam dake Enugu.

Nnolim Nnaji, shugaban kwamitin ne yayi wannan yabo inda ya ce abinda Buhari yayi dole ya dade a cikin zukatan jama’ar Kudu maso gabashin Najeriya.

KU KARANTA:Kogi : Kwamitin bincike ya mika rahotonsa a kan Simon Achuba ga majalisa

Idan baku manta ba dai, Shugaban kasan ya aminta da bayar da kudin nan ne bayan da gwamnonin yankin Igbo suka kai masa ziyara a Villa ranar Alhamis 17 ga watan Oktoba.

Nnaji ya sake fadin muhimmacin filin jirgin kasancewarsa shi ne kadai filin jirgin saman kasa da kasa dake yankin Kudu maso gabashin kasar nan.

Haka zalika, ya jinjinawa gwamnonin Kudu maso gabas da kuma shuwagabannin kungiyar Ohanaeze Ndigbo a kan kaiwa da komowa da suka yi tayi domin ganin an bada kudin wannan aikin.

Majiyar Daily Trust ta tattaro mana jawabin cewa, a cikin ‘yan kwanakin nan majalisar wakilai ta gayyaci ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika domin jin dalilin da yasa aka dakatar da aikin wanda aka fara tun 24 ga watan Agusta.

A karshen jawabinsa, Nnaji ya yabawa ministan sufurin jiragen saman a kan jajircewar da ya nuna wurin cigaban aikin filin jirgin saman Akamu Ibiam. Kuma yayi fatar yadda gwamnati ta bada kudi a gyara filin jirgin Enugun za ta mayar da hankali a kan sauran filayen jirgin dake kasar nan.

A wani labarin zaku ji cewa, kwamitin bincike a kan Simon Achuba mataimakin gwamnan jihar Kogi, ya mika rahoto ga majalisar dokokin jihar.

https://www.dailytrust.com.ng/reps-laud-n10bn-intervention-fund-for-enugu-airport.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel