Kogi : Kwamitin bincike ya mika rahotonsa a kan Simon Achuba ga majalisa

Kogi : Kwamitin bincike ya mika rahotonsa a kan Simon Achuba ga majalisa

Wani kwamitin binciken a kan zargin da ake yiwa mataimakin gwamnan Kogi Simon Achuba, wanda Barista John Baiyeshea ke jagoranta ya mika rahotonsa zuwa ga Majalisar jihar.

Alkalin alkalan jihar Kogi, Jastis Nasir Ajanah shi ne ya kafa wannan kwamitin. John kuma wanda shi ne shugaban kwamitin ya jagoranci mika rahoton binciken zuwa ga Kakakin majalisar jihar a ranar Juma’a 18 ga watan Oktoba, 2019.

KU KARANTA:Satar jarabawa: Kwalejin kimiyya da fasaha ta Nasarawa ta sallami dalibai 66

Kakakin majalisar, Kolawole Matthew ne ya karbi rahaton daga hannun shugaban kwamitin a Majalisar jihar dake Lokoja. Da yake magana bayan mika rahoton shugaban kwamitin ya ce sun yi iya bakin kokarinsu na yin bincike na gaskiya.

A cewar shugaban, John Baiyeshea, a shirye kwamitinsu yake domin amsa duk wata tambaya da ta sahfi abinda rahoton nasu ya kunsa. Kuma ya kara da cewa rahoton ya kasu zuwa mujalladi uku.

Haka zalika, ya bada shawara ga masu bukatar rahoton wadanda doka ta halarta masu mallakarsa da su bi hanyar da ta dace domin samunsa.

Da yake nasa jawabin bayan karbar rahoton, Kakakin majalisar jihar Kogi, Kolawole Matthew ya ce majalisa za ta yi bitar rahoton sannan kuma daga bisani za ta yanke hukunci a kan gaskiya.

Haka kuma, kakakin ya jinjinawa kwamitin a kan yin aikin da aka sanyasu cikin lokaci ba tare da neman taimakon wani ko wasu mutanen ba.

Daily Trust ta ruwaito cewa a ranar 26 ga watan Agusta, 2019 aka kafa kwamitin inda aka ba shi kwana 90 domin kawo rahoton binciken nasu.

https://www.dailytrust.com.ng/panel-investigating-kogi-deputy-gov-submits-report-to-assembly.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel