Boko Haram: Dakarun Sojin Najeriya sun cigaba da samun narasa a kan yan ta’adda

Boko Haram: Dakarun Sojin Najeriya sun cigaba da samun narasa a kan yan ta’adda

Dakarun rundunar Sojin Najeriya sun cigaba da samun nasara a kokarinsu na kawo karshen ayyukan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, musamman ma jahar Borno.

Rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito shugaban sashin watsa labaru na ayyukan tsaro na rundunar Sojan kasa, Kanal Aminu Iliyasu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Juma’a, 18 ga watan Oktoba a garin Abuja.

KU KARANTA: Gungun yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban makarantar Firamari a Kaduna

Iliyasu yace runduna ta 3 na Operation Lafiya Dole sun gano wasu bindigu guda 4 kirar AK 47, bindigar harba bamabamai guda 2, motar yaki da kuma babur guda daya, wanda mayakan Boko Haram suka jefar dasu yayin da suke tserewa daga Sojojin Najeriya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Iliyasu ya cigaba da cewa Sojoji sun fatattaki mayakan Boko Haram a garin Gubio tare da kashe mutum daya daga cikinsu, inda a nan ma sun kwato bindigar AK 47 guda 1, wayar hannu, allurai, da kuma na’urar sadarwa.

“Bugu da kari Sojojin runduna ta 231 sun kama wani dan Boko Haram mai suna Baana Zakari wanda ake yi ma inkiya da suna Okocha a tashar mota ta Biu, bincike ya nuna Baanaa yana sanar da kungiyar Boko Haram bayanan sirri.

“Sojojin runduna ta 231 sun kama wani mutumi dake kai ma Boko Haram kayan aiki mai suna Alhaji Lawan, wanda ake yi ma inkiya da Ceffenol a daidai shingen binciken ababen hawa dake Maina Hari. An kama shi ne yana kokarin kai ma Boko Haram kayayyaki.

“Daga cikin kayan da aka gano a hannunsa akwai jarakunan man ja, man gyada, katon biyu na biskit, taliyar spaghetti da kuma pakiti 30 na maganin sauro, kuma tuni Caffenol ya fara baiwa Sojoji muhimman bayanai.” Inji shi.

Daga karshe Iliyasu yace Sojoji sun sake kama wani dan ta’adda dake yi ma mayakan kungiyar ta’addanci na ISWAP hidima, mai suna Usman Yage, kuma bincike ya tabbatar da yana waya da manyan kwamandojin ISWAP da Boko Haram kamar su Goni Jere, Abul Qaqa da Modu Sulum.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel