Satar jarabawa: Kwalejin kimiyya da fasaha ta Nasarawa ta sallami dalibai 66

Satar jarabawa: Kwalejin kimiyya da fasaha ta Nasarawa ta sallami dalibai 66

Kwalejin gwamnatin tarayya ta kimiyya da fasaha dake Nasarawa ta kori dalibai 66 a dalilin samunsu da laifin satar amsa a lokacin jarabawa.

Shugaban kwalejin, Abdullahi Hassan ne ya bada wannan labarin inda ya ce, an dauki irin wannan matakin ne domin tabbatar da tarbiya da kuma dokokin kwalejin wurin bayar da ilimi mai inganci.

KU KARANTA:Yanzu-yanzu: 'Yan sanda sun tarwatsa dandazon 'ya shi'a da suka fito zanga-zanga a Abuja

Abdullahi ya ce daliban da aka korar sun hada da masu karatu na dogon zango da kuma masu karatu a kwaleji na dan takaitaccen zango. Hukumar gudanarwar kwalejin ce ta aminta da sallamar daliban, inji shi.

Shugaban makarantar ya ce: “An gama tsayar da maganar sallamar daliban ne a ranar Laraba 25 ga watan Satumba, 2019, bayan da hukumar gudanarwar makarantar ta zauna domin yanke hukunci a kansu.

“Ana umurtar dukkanin daliban da aka sallama da su maido da duk wani mallakin makarantar da yake a hannunsu. Wadannan abubuwan kuwa sun hada da, katinsu na makaranta gaba dayansu.” Inji shi.

Abdullahi ya sake jaddada aniyarsa ta ganin bayan magudin jarabawa a makarantar, inda ya ce babu shi babu hutu har sai ya ga bayan magudin jarabawa da ma wasu ayyuka masu kama da ita a makarantar.

A wani labarin kuwa, zaku ji cewa, ‘yan sanda sun fatattaki dandazon ‘yan shi’an da suka fito zanga-zanga a Abuja yau Juma’a da misalin karfe 1:55.

‘Yan shi’a dai sun fito ne suna dauke da tutoci bakake da jajaye, inda suke fadin “Labbaika ya Hussaini, a sako mana Zakzaky.” A kan titin Sultan Abubakar ne zanga-zangar ta fara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel